Matthew 16

Neman Alama

1Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yǎ nuna musu wata alama daga sama.

2Ya amsa ya ce,
Waɗansu rubuce rubucen hannu na farko farko ba su da raguwar aya 2 da kuma dukan aya 3.
“Saʼad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’
3da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokatai. 4Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa.

Yistin Farisiyawa da Sadukiyawa

5Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi. 6Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka tsantsan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

7Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, “Ko don ba mu kawo burodi ba ne.”

8Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba? 9Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike? 10Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka? 11Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.” 12Saʼan nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

Shaidar Bitrus a kan Kiristi

13Saʼad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?”

14Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Eliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.”

15Ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?”

16Siman Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Kiristi,
Ko kuwa Almasihu; haka ma a aya 20
Ɗan Allah mai rai.”

17Yesu ya amsa, ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama. 18Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,
Bitrus na nufin dutse.
a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hades
Ko kuwa lahira
ba za su rinjaye ta ba.
19Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka ɗaure a duniya zai zama a ɗaure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.” 20Saʼan nan ya gargaɗi almajiransa cewa kada su faɗa wa kowa shi ne Kiristi.

Yesu Ya Yi Zancen Mutuwarsa

21Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yǎ tafi Urushalima yǎ sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

22Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!”

23Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin alʼamuran Allah, sai dai alʼamuran mutane.”

24Saʼan nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bin na, dole yǎ ƙi kansa, yǎ ɗauki gicciyensa, yǎ bi ni. 25Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi. 26Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa? 27Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da malaʼikunsa, saʼan nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi. 28Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”

Copyright information for HauSRK